logo

HAUSA

Jami’in Najeriya ya bukaci a tsara dabarun yaki da cutar kwalara a lokacin damina

2022-05-11 11:38:34 CMG Hausa

Wani jami’i a Najeriya ya yi kira ga dukkan jahohin kasar da su samar da wani tsari tare da aiwatar da shirin kai dauki da kuma kandagarkin barkewar cutar kwalara a yayin da ake shirin shiga yanayin damina.

Ibiyemi Olu-Daniels, mataimakin darakta mai kula da sashen tsaftar ruwa a ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasar, ya bayyana a wajen wani taro game da tsaftar ruwa a Abuja, babban birnin kasar cewar, lokacin damina ya kasance a matsayin wani lokaci da ake samun yawaitar barkewar cututuka dake da alaka da tsaftar ruwa, kamar cutar amai da gudawa, da kwalara.

Olu-Daniels ya ce, ta hanyar ci gaba da shirin fadakarwa don wayar da kan al’umma, mai yiwuwa ne a shekarar 2022 a samu karancin masu kamuwa da cutar kwalarar idan an kwatanta da adadin barkewar cutar kwalara da aka samu a shekarar 2021, inda aka samu sama da masu kamuwa da cutar 110,000, da kuma adadin mutanen da cutar ta kashe kimanin 3,600 a jahohin kasar 33 da Abuja. (Ahmad)