logo

HAUSA

Kwararre: Alkawuran Da Aka Yi A FOCAC Yana Da Matukar Muhimmanci Wajen Yakar Talauci A Afirka

2022-05-11 20:28:38 CMG HAUSA

Wani kwararre kan manufofin diplomasiyya ya bayyana cewa, yayin da nahiyar Afirka ke kokarin fitar da miliyoyin jama'arta daga kangin talauci, alkawuran da aka yi a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) na iya taka muhimmiyar rawa.

Babban darektan cibiyar kula da harkokin raya kasa, dake nazarin manufofin da suka shafi harkokin diplomasiyya Allawi Ssemanda, ya bayyana a cikin wata makala da aka wallafa a jita Talata cewa, kasashen Afirka, za su iya daidaita tsarin kawar da talauci da hadin gwiwar Sin da Afirka waje guda

A yayin taron ministocin dandalin FOCAC karo na takwas da aka gudanar a kasar Senegal a watan Nuwamban bara, kasashen Afirka da Sin sun bayyana wasu fannoni guda 9 da Sin za ta tallafa .

Bangarorin guda tara sun hada da zaman lafiya da tsaro, da inganta kwarewar aiki, da hulda tsakanin al’ummu, da rage fatara da inganta kasuwanci da zuba jari. Sauran sassan su ne tallafawa shirye-shiryen kiwon lafiya, da aikin gona, kare muhalli da kirkire-kirkire na zamani.

Ssemanda ya ba da shawarar cewa, masu tsara manufofi, za su hada kai da kasar Sin ta fannonin da aka gano, domin rage tsananin talauci a nahiyar.

Yana mai cewa, yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki da fasaha da aka cimma a baya-bayan nan tsakanin Uganda da Sin, mataki ne da ya dace na inganta rayuwar jama'a. (Ibrahim)