logo

HAUSA

Amurka ta sake cusa matsalolinta ga sauran kasashen duniya

2022-05-11 13:59:31 CMG Hausa

A makon jiya ne, babban bankin tarayyar Amurka ya sanar da karu da mizanin kudin ruwansa 0.005, da ma rage basussukan da kasar ke bi daga watan Yuni mai zuwa, da nufin daidaita matsalar hauhawar farashi mafi tsanani da take fuskanta cikin shekaru 40 da suka gabata.

A hakika, tun bayan da Amurka ta ayyana yin babakere a duniya da dallarta, ta sha daukar matakin kwace dukiyoyin kasashe wato a yayin da take aiwatar da manufar kudi mai sassauci, tsarin ajiyar bankin ya kan rage kudin ruwa, ta yadda kasashen duniya za su kara karbar basusuka daga wajenta, tare da sa kaimin ci gaban tattalin arziki. A sa’i daya kuma, idan bankin ya kara kudin ruwan, to kudaden jari kan fita daga sauran kasashe, matakin da zai haifar da sauye-sauyen farashin musayar kudi da ma durkushewar tattalin arziki, har ma da rikicin hada-hadar kudi.

Abin lura a nan shi ne, bayan da Amurka ta shiga mawuyacin yanayin tattalin arziki, a maimakon ta yi tunani kan dalilin da ya haddasa hakan, sakamakon rashin daukar matakan da suka dace, amma sai ’yan siyasar Amurka suka fara daukar matakin da suka saba na dora laifinsu kan wasu, don cusa matsalolinsu ga wasu. Hakan tamkar rashin daukar nauyinsu ne na al’ummar Amurka da ma duk duniya baki daya. (Lubabatu Lei)