logo

HAUSA

Tsohon shugaban Najeriya ya yi watsi da takardun neman tsayar da shi takara da aka saya masa

2022-05-11 10:54:34 CMG Hausa

 

Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi watsi da takardun neman tsayar da shi takarar shugaba a zaben shekarar 2023 da aka saya masa.

Wata sanarwa da ofishin watsa labarai na tsohon shugaban kasar ya fitar ta bayyana cewa, a ranar Litinin, wasu rukunin mutane suka gabatarwa Mr. Jonathan takardun neman shiga takarar, karkashin jam’iyyar APC mai mulki, jam’iyyar da ita ce ta kada shi a babban zaben kasar na shekarar 2015, bayan ya shafe shekaru 5 a kan karagar mulkin kasar.

Akwai dai tarin ’yan siyasar kasar dake fatan maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari, bayan kada kuri’un babban zaben kasar dake tafe, wanda suke sayen takardun neman a tsayar da su takara ta hannun wasu makusantan su.

Sanarwar ta ce tsohon shugaban Najeriyar, bai taba nuna bukatar wani rukuni ya saya masa takardun nuna sha’awar neman takarar zaben dake tafe a watan Fabarairun shekarar badi ba.

Nan gaba cikin wannan wata ne, ake sa ran manyan jam’iyyun Najeriyar APC da PDP, za su kammala tantance wadanda za su tsaya musu takarar shugabancin kasar, gabanin wa’adin karshe na farkon watan Yuni, da hukumar zaben kasar mai zaman kan ta INEC ta ayyana.  (Saminu)