logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci kasashe mafiya karfi da su yi alkawarin kauracewa neman yin babakere a sararin samaniya

2022-05-11 12:12:51 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin mai kula da harkokin kwance damara, Mr. Li Song ya halarci taron da MDD ta shirya a ofishin ta na birnin Geneva a jiya Talata, inda ya bayyana matsayin kasar Sin kan yanayin tsaron sararin samaniya, da ma bukatar kauracewa takarar kafa makamai a sararin samaniya, tare da yin kira ga gamayyar kasa da kasa da su dukufa wajen kiyaye tsaron bai daya a sararin samaniya.

Jakada Li ya jaddada cewa, aikin da ya rataya a wuyan kasashe mafiya karfi shi ne su yi alkawarin yin watsi da neman yin babakere a harkokin sararin samaniya. Ya yi nuni da cewa,“Na farko, ya kamata a kiyaye tsaro na bai daya a sararin samaniya. Bai kamata wata kasa ta lalata tsaro na wasu kasashe domin kiyaye tsaron kanta ba, kuma bai kamata a yi ‘takarar manyan kasashe’ a sararin samaniya, da kafa kawance, ko kuma rura kiyayya a tsakanin kasashe daban daban a harkokin sararin samaniya. A maimakon haka, ya kamata kasa da kasa su hada kai wajen tinkarar barazana da ake fuskanta, ta fannin tsaron sararin samaniya. Na biyu, ya kamata a magance yin takarar mallakar makamai a sararin samaniya. Ko za a nuna goyon baya ga yin shawarwari don cimma yarjejeniyar kayyade mallakar makamai a sararin samaniya, abu ne da zai gwada ko wata kasa za ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta ko a’a. Na uku, ya kamata a tabbatar da hakkin kasa da kasa wajen gudanar da harkokinsu a sararin samaniya cikin daidaito, musamman ma a kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, domin bai kamata a hana harkokin da wata kasa ke son gudanarwa a sararin samaniya yadda ya kamata bisa hujjar wai ‘ta haddasa barazanar tsaro’ ba. Na hudu, ya kamata a goyi bayan MDD, wajen taka rawar jagoranci, a fannin kula da harkokin sararin samaniya, ta yadda za a kiyaye wakilcin kasa da kasa, da ma adalci, wajen tsara dokokin kasa da kasa kan harkokin sararin samaniya, don kada wasu kasashe kalilan su tilastawa sauran kasashe bin ra’ayinsu.”(Lubabatu)