logo

HAUSA

Kasar Sin ta kafa tashar binciken yanayi mai sarrafa kanta mafi tsayi a duniya

2022-05-11 09:00:04 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, masu binciken kimiyya na kasar Sin suka yi nasarar kafa tashar sanya ido kan yanayi mai sarrafa kanta a tsawon mita 8,830 a kan tsaunin Qomolangma dake kan iyakar Sin da Nepal, abin da ya sanya ta zama mafi tsayi irinta a duniya.

A cewar cibiyar binciken tsaunin Tibet (ITP) dake karkashin cibiyar kimiyya ta kasar Sin (CAS), tashar ta maye gurbin tashar da aka kafa a tsayin mita 8,430 a gefen kudu da dutsen, wanda masana kimiya na kasashen Birtaniya da Amurka suka kafa a shekarar 2019, a matsayin mafi tsayi a duniya a wancan lokaci,

Baya ga sabuwar tashar nazarin yanayi, an kuma kafa kananan tashoshin sanya ido kan yanayi guda takwas a kan tsaunin na Qomolangma, daya daga cikin manyan ayyuka a jerin sabon aikin binciken kimiyya na kasar Sin, a kan kololuwar tsayin mita 8,848.86 da babu kamarsa a duniya. 

Ita dai wannan tawagar masu bincike na kasar Sin mai mambobi 14 tana dauke da tashoshin bincike yanayi masu sarrafa kansa da na'urorin radar, kuma rahotanni na cewa, wannan ita ce tafiya mafi muhimmanci da tawagar kwararrun masu hawan tsauni suka gudanar kan wannan manufa.

Masana na cewa, bayanan yanayin da za a tattara, za su taimaka ga ayyukan binciken kimiyya da hawan duwatsu. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)