logo

HAUSA

Shin Amurka Adawa Take Da Kasar Sin Ko Da Ci Gaban Nahiyar Afrika?

2022-05-10 18:35:40 CMG Hausa

A baya bayan nan, yayin ziyararta a nahiyar Afrika,mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka Wendy Sherman,ta bayyana cewa, wasu kasashen Afirka sun zabi kamfanin Huawei na kasar Sin a matsayin kamfanin dake samar da hidimar sadarwa.  Tana mai cewa wai wadannan kasashe sun yi watsi da ikon mulkin kai. 

Yaushe neman ci gaba ya taba zama watsi da 'yancin kai? Shin wannan adawa ne da kasar Sin karara ko kuma adawa ne da ci gaban nahiyar Afrika? Shin ita Amurkar ta gabatar da wani kamfani mai bada hidima cikin sauki ne kamar kamfanin Huawei? Ko kuma ta samarwa kasashen na Afrika wasu hanyoyi na daban na samun ci gaban sadarwa?

Amurka ta dade tana daukar kamfanin Huawei a matsayin abokiyar adawa, bisa  la’akari da yadda ta yi ta yi wa kamfanin da shugabaninta bita da kulli. Amma duk wannan bai ishe ta ba, tana nema ta ingiza rikici tsakanin kamfanin da kasashen Afrika.

Kasashen yammacin duniya sun dade suna yin watsi da damarsu a Afrika, yanzu kuma suna kokarin shiga tsakanin Sin da kasashen Afrika ganin yadda Sin din ta samu karbuwa a nahiyar. Tuni kan kasashen Afrika ya riga ya waye, sun gane inda za su samu hadin gwiwar moriyar juna ba tare da wani sharadi ko katsalandan cikin harkokinsu na gida ko tsawalla kudin ruwa ko ci da guminsu ba. A matsayin da take ganin kanta na babbar kasa, ba girman Amurka da jami’anta ba ne su rika sukar kasar Sin kan dangantakarta da kasashen Afrika.

Kamata ma ya yi a jinjinawa kasar Sin da kamfanoninta da suka dukufa wajen inganta huldar kasa da kasa da kuma tabbatar da ganin ba a bar kasashen Afrika a baya yayin da ake fafutukar neman ci gaba a duniya ba. Kowacce babbar kasa kanta ta sani da moriyarta, amma kasar Sin ta fita daban, inda take neman ci gaba tare da kokarin jan kasashen Afrika a jikinta. (Fa’iza Mustapha)