logo

HAUSA

Yemi Osinbajo: Afirka na bukatar karfafa matakan samar da isashen abinci

2022-05-10 11:02:53 CMG HAUSA

 

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Yemi Osinbajo ya ce, nahiyar Afirka na da bukatar karfafa matakan cimma nasarar samar da isashen abinci, wanda al’ummun take bukata.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin taron karawa juna sani na jagorori da manyan jami’an majalisun dokokin kasashen Afirka, wanda ya gudana a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya. Ya kalubalanci kasashen Afirka da su zage damtse wajen noman abun da zai ishe su, tare da rage dogaro ga kasashen waje a fannin cimaka.

Ya ce annobar COVID-19 ta haifar da karancin abinci ga sassan Afirka, wanda hakan ke kara fito da bukatar fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen nahiyar, wajen shawo kan wannan kalubale, ciki har da cimma nasarar noma isasshen abinci.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa, nahiyar Afirka ta yi namijin kokari, wajen shawo kan cutar COVID-19, sai dai kuma har yanzu, tana dandana kudar ta daga tasirin annobar a fannonin zamantakewa da tattalin arziki.

Daga nan sai ya shaidawa mahalarta taron cewa, annobar ta kara fito da muhimmancin manufofin baiwa al’umma kariya, don haka kamata ya yi kasashen Afirka su yi amfani da darashin da suka koya yayin annobar, wajen aiwatar da matakan inganta tsarin kiwon lafiya.  (Saminu)