logo

HAUSA

Malaman jami’o’in Najeriya sun tsawaita yajin aikin gama gari da suke a halin yanzu

2022-05-10 10:53:48 CMG HAUSA

 

Shugaban kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU, Emmanuel Osodeke, ya sanar a ranar Litinin cewa, malaman dake koyarwa a makarantun gwamnatin kasar sun tsawaita wa’adin yajin aikin da suke da makonni 12.

A sanarwar da aka fitar an ce, an dauki wannan mataki ne, domin baiwa gwamnatin kasar isasshen lokaci don warware dukkan batutuwan da malaman suka jima suna muhawara kansu, karkashin jagorancin kungiyar malaman jami’o’in ta ASUU, an kuma bukaci gwamnatin ta gaggauta warware dukkan matsalolin da aka gabatar, wadanda ke kunshe cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin da ASUU a shekarar 2020. 

ASUU ta fara yajin aikin gama gari ne a watan Fabrairun wannan shekara, inda ta gabatar da wasu bukatu da suka hada da neman kyautata yanayin aikin koyarwa, da neman gwamnati ta samar da kudaden da za a inganta makarantun gwammatin kasar, kana a biya kudaden alawus da na karin girma da malaman ke bin gwamnatin.

Kawo yanzu dai ba a kawo karshen tattaunawar dake gudana tsakanin gwamnatin da kungiyar ASUU ba, don a samu maslahar kawo karshen yajin aikin da malaman jami’o’in suka tsunduna cikinsa. (Ahmad)