logo

HAUSA

Zhu Huishan: aikin fentin motoci wani aiki ne mai launuka daban daban

2022-05-10 20:11:05 CMG HAUSA

Zhu Huishan, wadda aka haife ta a shekarun 2000, ta yi aikin fentin motoci a wani babban kamfanin kera motoci na kasar Sin. A yayin da take karatu a kwalejin koyar da sana’a, ta samu lambar yabo yayin gasar fid da gwani a fagen fasaha ta kasar Sin karo na farko a shekarar 2020. Zhu Huishan ta ayyana aikin fentin motoci a matsayin wani aiki mai launuka daban daban da kuma mai ban sha’awa. Ta yi fatan cewa, za ta ba da gudummowa wajen inganta sha’anin fentin motoci zuwa matsayi mafi girma. (Tasallah Yuan)