logo

HAUSA

Sanarwar kasashen yamma game da zaben gwamnan HK abin dariya ne

2022-05-10 16:25:14 CMG Hausa

Jiya Litinin ministocin harkokin wajen kasashen rukunin G7 wato Amurka da Birtaniya da Jamus da Italiya da Japan da Faransa da Canada da babban wakilin tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa game da zaben gwamnan Hong Kong, yankin musamman na kasar Sin karo na bakwai da aka gudanar a ranar 8 ga wata. A bayyane take, an lura cewa, sanarwar ta kasance tamkar wani makirci ne mai ban dariya, idan aka fahimci hakikanin yadda zaben ya gudana.

An gudanar da zaben ne bisa adalci, inda aka kara adadin mambobin kwamitin zaben daga 1200 zuwa 1500 bisa sabon tsarin dokar zaben da aka tsara, domin tabbatar da moriyar dukkanin mazauna yankin na Hong Kong, kana adadin kuri’un da aka jefa ya kai kaso 97.74 bisa dari, adadin da ya kai matsayin koli a yankin, tun bayan da aka maido da yankin karkashin mulkin kasar Sin a shekarar 1997, har yawan kuri’un da aka jefawa zababben gwamna Lee Ka-chiu sun kai kaso 99.16 bisa dari, adadin da ya kasance mafi yawa idan an kwatanta da na sauran gwamnonin yankin a baya.

Ana iya cewa, zabuka uku da aka gudanar, wato zaben mambobin kwamitin zabe, da zaben kwamitin kafa dokoki karo na bakwai, da zaben gwamnan yankin sun aza harsashe mai kyau ga zaman lafiyar yankin Hong Kong cikin dogon lokaci, su ma sun shaida cewa, sabon tsarin zaben, tsarin demokuradiya ne da ya dace da ka’idar “kasar Sin daya mai tsarin mulki iri biyu”.

Kuma dai mene ne wasu kasashen yamma suke furtawa domin neman shafawa yankin kashin kaji, bai zai taba yiwuwa su hana ci gaban yankin ba. (Jamila)