logo

HAUSA

Charles Onunaiju: Muzgunawa tsirarun al’ummu a Amurka alamu ne na dadaddiyar dabi’ar nuna wariyar launin fata

2022-05-10 14:24:56 CMG HAUSA

Masanin harkokin kasa da kasa a Najeriya Charles Onunaiju ya ce, kisan wani matashi mai shekaru 26, dan asalin Congo da wani dan sanda farar fata ya yi a jihar Michigan ta Amurka a baya bayan nan, na nuni ga dadaddiyar dabi’ar nuna wariyar launin fata da ta yi katutu a Amurka.

Cikin wata makalarsa da aka wallafa a jaridar Blueprint, Charles Onunaiju ya ce, duk da bacin rai, da adawar da al’ummun duniya suka nuna don gane da kisan da wani dan sanda farar fata ya yiwa bakar fata George Floyd, a watan Mayun shekarar 2020, har yanzu ba ta canza zani ba, domin kuwa har yanzu ’yan sandan Amurka fararen fata, na ci gaba da muzgunawa, da nuna karfin tuwo kan Amurkawa ’yan asalin Afirka, ko bakaken fata mazauna kasar.

Onunaiju ya kara da cewa, tsarin ayyukan ’yan sanda a Amurka, na tattare da ci gaba da muzgunawa al’ummu marasa rinjaye, musamman ma ’yan asalin Afirka dake kasar.

Daga nan sai masanin ya ja hankalin gwamnatocin Afirka, da sauran muryoyin nahiyar, ciki har da jam’iyyun siyasa, da kungiyoyin kwadago, da sauran jam’iyyun gama kai, da su maida hankali ga ’yancin Amurkawa bakaken fata, wadanda ke fuskantar cin zarafi da muzgunawa daga ’yan sandan Amurka. (Saminu)