logo

HAUSA

Habasha ta sanar da kara farashin albarkatun mai

2022-05-09 10:42:44 CMG Hausa

 

Ma’aikatar kula da cinikayya da dunkulewar yanki ta kasar Habasha, ta sanar da matakin kara farashin gas da kaso 16, daga jiya Lahadi.

Ma’aikatar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Asabar. Tana mai cewa, farashin gas zai tashi daga Birr 31.74, kwatankwacin US cents 62, zuwa Birr 36.87 kan kowacce lita.

Haka zalika, karin farashin zai shafi man diesel, inda zai tashi daga Birr 28.98 zuwa Birr 35.43.

Gwamnatin Habasha ta ce karin farashin albarkatun mai ya zo ne bayan jinkirta daukar matakin na tsawon watanni 4 da suka gabata.

Ma’aikatar ta dora alhakin daukar matakin ne kan karuwar farashin mai a duniya. A cewarta, lura da yanayin rayuwar jama’a ne ya sa ba ta yi karin ba cikin watanni 4 da suka gabata. Sai dai, hakan ya kai gwamnati ga samun gibi Birr biliyan 10, wanda ya kamata a ce masu amfani da albarkatun ne ke biya, lamarin da ya haifarwa gwamnatin da matsin kudi.

Har ila yau, ma’aikatar ta ce za ta dauki mataki kan wadanda ke amfani da karuwar farashin wajen kawo karancin mai da gangan, da kara farashin muhimman kayayyaki.

Bisa alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar, an ce, hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya karu zuwa kaso 36.6 a watan Afrilu, daga kaso 34.7 da ya kasance a watan Maris. (Fa’iza Mustapha)