logo

HAUSA

Gwamnatin Sudan ta yi Allah wadai da harin da aka yi a Sinai na kasar Masar

2022-05-09 11:24:30 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta yi Allah wadai da harin wasu da ta kira ’yan ta’adda, kan rukunin sojojin kasar Masar mai makwaftaka, harin da ya sabbaba kisan sojojin Masar din su 11, a yankin gabashin gabar mashigin ruwan Suez.

Cikin wata nasarwa da ma’aikatar harkokin wajen Sudan din ta fitar a jiya Lahadi, ta tabbatar da goyon bayanta ga gwamnatin Masar, da ma yunkurin kasar na dakile duk wani nau’in ta’addanci.

Sanarwar ta ce harin na matsorata, ba zai karya kashin bayan gwamnatin Masar ba, da ma kokarin da kasar ke yi na baiwa al’ummar ta tsaro da wanzar da zaman lafiya.

A ranar Asabar ne wasu da ake zaton mayakan wata kungiyar ta’addanci ne, suka farwa rukunin sojoji dake aiki a wata cibiyar tace ruwa dake yammacin yankin Sinai, inda nan take suka hallaka sojoji a kalla 11, tare da jikkata wasu 5. (Saminu Hassan)