logo

HAUSA

Amurka Ta Aikata Ashsha Da Sunan Asusun NED

2022-05-09 21:40:25 CMG HAUSA

Kila wasu sun san asusun demokuradiyya na kasar Amurka, saboda sunan asusun ya ambato demokuradiyya wato NED. Amma mene ne gaskiyar asusun? Kwanan baya, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wasu jerin shaidu a shafinta na Internet, inda ta bankado asirin asusun. Hakika asusun NED ya kulla makarkashiya da yawa a sassan duniya, kamar ta da rikicin kawo baraka, yin juya juyin mulki, rikicin siyasa, yin karya da yada jita-jita da dai sauransu. Ba za a iya lissafa laifuffukan da asusun na NED ya aikata ba. Kila ayyukan ashsha da ya aikata za su wuce zaton mutane.

An kafa asusun NED a matsayin kungiya mai zaman kanta a shekarar 1983, da sunan bai wa kasashen duniya tallafin demokuradiyya, amma a hakika yana gudanar da aikace-aikacen na keta tsarin demokuradiyya.

Kasar Sin tana daya daga cikin wuraren da asusun NED ya fadada aikin makircinsa. Inda ya rura wutar fitina dangane da batutuwan Hong Kong, Taiwan, Xinjiang da Tibet.

Dimbin shaidu na zahiri sun nuna cewa, Amurka ta fake da asusun NED, tana tsoma baki a harkokin cikin gida na wasu kasashe, a kokarin samun moriya. Asusun ba ya kokarin shimfida demokuradiyya, illa yunkurin hambarar da gwamnatin wasu kasashe da kawo musu baraka, ta yadda Amurka za ta samu riba, har ma ta ci gaba da yin danniya a duniya. (Tasallah Yuan)