Kasashen Afirka Sun Yi Shiru Don Nuna Kin Amincewa Ga Kasashen Yamma
2022-05-09 21:43:54 CMG Hausa
Bayan barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine, Amurka da wasu kasashen yamma na kokarin mai da kasar Rasha saniyar ware, inda suke matsawa sauran kasashe lamba, domin su goyi bayansu. Hakan ya sa wasu jami’an kasar Amurka ke daga murya ga kasashen Afirka, don su yi watsi da matsayinsu na ‘yan ba ruwanmu. Duk da haka, yayin da ake jefa kuri’a a Majalisar Dinkin Duniya don tabbatar da cewa ko za a yi Allah wadai da kasar Rasha, akwai kasashe 25 dake nahiyar Afirka da suka jefa kuri’ar janyewa daga batun, ko kuma kin jefa kuri’ar.
To, me ya sa wadannan kasashen Afirka suka yi shiru duk da matsin lambar da su kasashen yamma suke yi?
Saboda da farko dai, ko da yake rikicin Rasha da Ukraine na nisa da nahiyar Afirka, amma yana jefa al’ummar Afirka cikin wahala sosai.
Yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine ya sa kasashen Afirka fuskantar matsalar karanci, da hauhawar farashin abinci, inda farashin alkama ya riga ya karu da kashi 60%. Baya ga yadda yaki yake tsananta matsalolin da Afirka ke fuskantar, a fannonin makamashi, da hada-hadar kudi. Amurka da sauran kasashen Turai na kokarin tura makamai ga kasar Ukraine, don neman raunata kasar Rasha bisa dorewar yake-yake. Sai dai hakan ba zai amfani kasashen Afirka ba, domin dorewar yakin ita ma za ta cusa kasashen Afirka cikin wahala matuka.
Ban da haka kuma, yadda su kasashen Afirka suka ki goyon bayan kasashen yamma, shi ma ya shafi wasu ayyukan da kungiyar tsaro ta NATO ta yi a baya.
Jama’ar kasashen Afirka ba za su manta da shishigin da sojojin kasashen NATO suka yi a kasar Libya ba, lamarin da ya sa kasar ta tsunduma cikin yanayi na rikici. Kana wannan yanayi ya haifar da ta’addanci. Bayan da aka hambarar da gwamnatin Ghaddafi, kasar Libya na ta fama da matsalar hare-haren ‘yan ta’adda, kana wannan matsala na yaduwa zuwa kasashe makwabtan kasar cikin sauri. Zuwa yanzu, jama’ar kasashen Najeriya, da Nijar, da Mali, da sauransu, suna shan wahalar hare-haren ta’addanci da ‘yan fashi, kuma asalin wadannan matsaloli shi ne yaki “na adalci” da kungiyar NATO ta kaddamar a kasar Libya a shekarar 2011. Hakika kungiyar NATO ita ma tana da hannu cikin yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine. Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya taba bayyana cewa, akwai damar magance yaki, idan har kungiyar NATO ta yi hakuri da kwadayinta na fadada zuwa yankunan gabashin duniya.
Sa’an nan yadda kasashen Afirka suka juya baya ga kasashen yamma a wannan karo, shi ma ya nuna takaicinsu kan bambancin da kasashen yamma suka nuna musu.
Bayan barkewar yaki a Ukraine, yayin da al’ummomin kasashen Afirka da suke zama a kasar suka yi kokarin ficewa, akwai wasu ‘yan kasar Ukraine da Poland da suka nuna musu kyama da wulakanci a lokacin. Ko da yake kasar Amurka tana neman dukkan kasashen duniya su yi Allah wadai da kasar Rasha, amma ta yi shiru game da abubuwan da Ukraine da Poland suka yi na nuna bambancin launin fata. A nata bangare, gwamnatin kasar Birtaniya ta yi alkawarin karbar ‘yan gudun hijira dubu 200 daga kasar Ukraine, yayin da a lokaci daya kuma take neman tusa keyar ‘yan gudun hijira daga nahiyar Afirka, don su koma kasar Rwanda dake nahiyar Afirka.
Ganin yadda kasashen yammacin duniya suke kokarin daukar manufofi na son kai, ya sa kasashen Afirka yin shiru game da bukatunsu. Hakan ya nuna ra’ayin kasashen Afirka, wato ba za su ci gaba da biyayya ga maslahar kasashen yamma ba, inda za su dauki manufar da za ta tabbatar da moriyarsu, bisa son ransu. (Bello Wang)