Juma’ar da za ta yi kyau daga Laraba ake gane ta
2022-05-09 16:16:15 CMG Hausa
Duk da irin yanayin da duniya ta tsinci kanta na yanayin tangal-tangal da rashin tabbas, kama daga batun matsalar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, wacce ta zamewa duniya babbar barazana, da matsin tattalin arziki, da matsalolin rikice-rikicen a sassan duniya, da matsalar sauyin yanayi da makamantansu. Sai dai a bisa dukkan alamu, za mu iya cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana nuna alamu masu kayatarwa kamar yadda hukumomin kasar suka nuna, a cikin kwanakin baya bayan nan da suka gabata, dukkanin larduna da birane 31 na kasar Sin sun fitar da ma’aunin ci gaban tattalin arziki wato GDP a rubu’in farko na bana, inda alkaluma suka nuna cewa, sassa daban daban na kasar sun samu ci gaba mai inganci yadda ya kamata, duk da cewa ana fama da matsin lamba da sauye-sauyen yanayin gida da na kasa da kasa ke haifarwa. A cikin watanni uku na farkon bana, adadin GDP na larduna 11 dake hade da lardin Guangdong ya zarta kudin Sin yuan triliyan daya, amma a makamancin lokacin bara, adadin GDPn lardunan ya karu ne da triliyan daya 8. Kana game da saurin ci gaban tattalin arziki kuwa, ban da lardin Jilin, wanda ke fuskantar tasirin yaduwar annobar COVID-19, sauran larduna da birane 30 dake fadin kasar sun samu karuwar tattalin arziki a rubu’in farkon bana, inda wasu lardunan dake tsakiya da yammacin kasar wadanda ke kunshe da Hubei da Shanxi da Xinjiang da Guizhou sun samu ci gaba cikin sauri inda saurin har ya kai kaso 6 cikin dari bisa makamancin lokacin bara. A karshen wannan mako, mataimakin shugaban cibiyar nazarin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare ta kasar Sin Wu Sa, ya bayyana cewa, duk da cewa tattalin arzikin yankunan gabashin kasar ba su samu ci gaba cikin sauri ba, amma suna samun ci gaba mai inganci sannu a hankali. Don haka za mu iya cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu tagomashi tun daga rubu’in farko na bana, kuma hakan wasu alamu ne dake nuni da cewa, tamkar batun nan ne da masu hikimar magana ke cewa, “Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta.” (Ahmad Fagam)