logo

HAUSA

Ya Fi Kyau ‘Yan Siyasar Birtaniya Su Mai Da Hankali Kan Harkokinsu

2022-05-08 20:40:08 CMG HAUSA

Ranar 7 ga wata, an kaddamar da sakamakon zaben kananan hukumomi a Northern Ireland na kasar Birtaniya, inda jam’iyyar Sinn Féin da ke neman raba Northern Ireland daga Birtaniya ta fi samun kujeru, ta zama jam’iyya mai kare muradun al’umma da ta fi samun kujeru a majalisar dokokin Northern Ireland cikin shekaru 101 da suka wuce. Manazarta sun yi bayani cewa, nasarar da jam’iyyar Sinn Féin ta samu ta bai wa gwamnatin Birtaniya wata matsala ta daban.

Bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, gwamnatin Birtaniya ta yi kasala wajen yaki da annobar. A watan Febrairun bana, ta sanar da mayar da annobar a matsayin wani nau’in cuta mai kamawa, a maimakon mummunar cuta mai kamawa, lamarin da ya sa jimillar yawan mutanen da suka mutu sakamakon annobar ya kai kusan dubu 180 a Birtaniya.

Ban da haka kuma, Birtaniya na fuskantar matsaloli da dama wajen raya tattalin arziki sakamakon annobar, da matsala a tsarin samar da kaya, da karancin ‘yan kwadago, sakamakon janye kanta daga kungiyar EU da kuma hauhawar farashin makamashi. A ranar 5 ga wata, bankin Ingila ya yi kashedin cewa, a bana yawan hauhawar farashin kaya zai iya wuce kashi 10% a Birtaniya. An kiyasta cerwa, adadin zai kafa tarihi cikin shekaru 40 da suka gabata. Kila tattalin arzikin kasar zai samu koma baya a shekara mai zuwa.

Amma yayin da wadanda ke mulkin kasar suke fuskantar wahalhalu a gida da wajen Birtaniya, sun yi yunkurin nuna karfi ga kasashen duniya a maimakon yin tunani kan matakan da za a dauka. Ya fi kyau ‘yan siyasar Birtaniya su mai da hankali kan harkokinsu. (Tasallah Yuan)