logo

HAUSA

Shugaban Masar ya yi ta’aziyyar wadanda suka mutu a harin Sinai

2022-05-08 17:20:06 CMG HAUSA

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya nuna jejeto ga mutanen kasar Masar da rundunar sojojin kasar bayan wani harin da aka kaddamar a yankin Sinai wanda ya yi sanadiyyar hallaka dakarun sojojin kasar 11.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, shugaban kasar ta Masar ya ce, yana ba da tabbacin wannan mummunan aikin ‘yan ta’adda ba zai taba kashe gwiwa da kuma hana cikar burin ‘yan kasar, da kuma ayyukan da dakarun kasar ke yi na yaki da ‘yan ta’adda ba.

Abdel-Fattah al-Sisi ya kuma yaba da kokari da sadaukar da kai da sojojin kasar suka nuna a yaki da ayyukan ta’addanci.

Tun da farko a wannan rana, an ba da rahoton mutuwar dakarun kasar Masar a kalla 11, tare da raunata wasu 5, a yayin da suka fafata da kungiyoyin ‘yan ta’adda a wata tashar samar da ruwa dake yammacin yankin Sinai, kamar yadda bangaren rundunar sojojin kasar suka bayyana cikin wata sanarwa, sannan sojojin suna ci gaba da kai samammen ‘yan ta’addan a wani wuri.

Ko da yake, sanarwar ba ta bayyana hakikanin wurin ba, sai dai shafin intanet na kamfanin dillancin labarai mallakin gwamnatin kasar na Al-Ahram ya ba da rahoton cewa, an yi artabun ne a wani wajen binciken ababen hawa dake gabashin tashar samar da ruwa ta East Canal.(Ahmad)