logo

HAUSA

MDD ta bukaci a kai daukin gaggawa na irin shuka da takin zamani ga yankunan da rikici ya shafa a arewacin Habasha

2022-05-08 17:33:14 CMG HAUSA

 

Ranar 7 ga wata, ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD (UNOCHA), ya yi kiran a samar da irin shuka da takin zamani ga manoma a yankunan da rikici ya shafa a arewacin kasar Habasha gabanin saukar damina.

UNOCHA ya bayyana a cikin wata sanarwa ta baya-bayan nan game da halin da ake ciki a yankunan cewa, yanayin da ake ciki game da bukatun jin kai a arewacin Habasha ya yi matukar tsananta, yayin da MDD ke ci gaba da yin aiki tare da dukkan sassa masu ruwa da tsaki domin samar da karin kayayyakin da ake bukata a yankunan Tigray, da Afar, da Amhara.

Mafi akasari, damina a kasar Habasha tana farawa ne daga watan Yuni zuwa Satumba a ko wace shekara, inda ake samun kashi 85 zuwa 95 cikin dari na abinci da kasar ke bukata, kamar yadda alkaluman da gwamnatin kasar ta fidda suka nuna.

Ofishin na UNOCHA ya yi gargadin cewa, muddin aka gaza samar da irin shukar da takin zamanin, lamarin zai iya kasancewa mafi muni da za a fuskanta na rashin kyawun damina a karo na uku a jere a yankunan da rikicin ya shafa.

A yankin Tigray, UNOCHA ya ce, ana bukatar takin zamani ton 60,000, da ton 50,000 na sabbin nau’ikan irin shuka, da maganin kashe kwari lita 40,000 da maganin kashe kwayoyi lita 34,000. Bugu da kari, ana bukatar riga-kafi, da magunguna da kayayyaki ga dabbobin gida da yawansu ya kai miliyan 12.

A yankin Amhara, manoma miliyan 3.3 suna bukatar tallafin a bangarori daban-daban na ayyukan gona, daga cikin adadin, manoma miliyan 2.6 na bukatar ninkin tallafin a fannin ayyukan gona.(Ahmad)