logo

HAUSA

Karancin kuzarin hannu yana da alaka da karancin tunani, da gushewar hankalin tsoffin Amurkawa

2022-05-08 15:36:17 CMG HAUSA

 

Manazarta daga jami’ar Michigan (UM), da jami’ar North Dakota a kasar Amurka, sun gano cewa, kila raguwar kuzarin hannu, wata alama ce ta lalacewar kwarewar fahimta da rikon abubuwa.

Masu nazarin sun dauki shekaru 8 suna bibiyar mutane kusan 14,000 ‘yan shekaru 50 da haihuwa, wadanda suka shiga wani nazari da aka gudanar a shekarar 2006 dangane da lafiyar mutane da kuma yin ritaya daga aiki.

A cewar rahoton bincike wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na jami’ar Michigan, masu nazarin sun binciki mutanen ne ta hanyar amfani da wata na’urar auna kuzarin hannu da kuma gudanar da wani karamin bincike kan kwarewar mutane ta fahimta, wanda aka yi sau da yawa tsakanin tsoffafi, ya hada da tabbatar da kwatance, da kwarewar mai da hankali kan abubuwa, da riko da abubuwa, da kuma kwarewar bambanta abubuwa.

Masu nazarin sun gano cewa, duk wata raguwar kuzarin hannu da aka samu da ta kai kilogram 5, to, yiwuwar samun matsalar fahimta za ta karu da kashi 10 cikin kashi 100, kana kuma yiwuwar samun mummunar matsalar fahimta za ta karu da kashi 18 cikin kashi 100.

Abu mafi muhimmanci shi ne, masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, raguwar da ake samu ta kuzarin hannu, tana da alaka da gushewar jijiyoyin kwakwalwar mutane, lamarin da ya kara fito da muhimmancin motsa jiki a fili.

Binciken wanda Sheria Robinson-Lane, mataimakiyar farfesa a sashen nazarin aikin jinya ta jami’ar Michigan ta jagoranta tare da hadin gwiwar wasu, ta bayyana cewa, wadannan sakamakon nazari da aka samu sun nuna cewa, motsa jiki zai yi tasiri kan cikakkiyar lafiyar dan Adam da kuma lafiyar tunaninsa.

A cewar mawallafin rahoton nazarin na farko Ryan McGrath, mataimakin farfesa a jami’ar jahar North Dakota, sakamakon nazarin ya ba da gaggarumar gudummawa dake tabbatar da abubwan dake shaida cewa, ya kamata a shigar da batun auna kuzarin hannun tsoffafi, wanda ba a amfani da shi a halin yanzu, cikin tsarin binciken yanayin lafiyar tsoffi.