logo

HAUSA

Duniya na bukatar sa ido kan ‘yan siyasar Japan dake neman daukar matakan soji

2022-05-07 20:03:43 CMG Hausa

A bana ake cika shekaru 75 da aiwatar da kundin tsarin zaman lafiya na Japan. Sai dai, wasu jerin abubuwan da ‘yan siyasar kasar ke yi sun nuna yadda suke kaucewa hanyar zaman lafiya da neman yi wa kundin tsarin katsalandan ta hanyar ruruta cewa kasar na fuskantar barazana daga waje, a yunkurinsu na neman Japan ta kafa rundunarta na tsaron kasa da samun damar tada yaki. Ya kamata kasa da kasa su kwan da sanin cewa wasu ‘yan siyasar Japan na neman aiwatar da matakan soji. (Fa’iza)