logo

HAUSA

Rundunar ‘yan sanda Nijeriya ta cafke mutane 46 da ake zargi da aikata laifuffuka

2022-05-07 19:38:08 CMG Hausa

 

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta cafke mutane 46 da ake zargin masu laifi ne, a ayyukanta na baya-bayan nan dake da nufin dakile ayyukan bata gari a jihar Enugu dake kudancin kasar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu, Lawal Abubakar, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an kama mutanen ne, bisa zarginsu da laifuka daban-daban da suka hada da kisa da fyade da satar mutane da hada baki da fashi da makami da mallakar makamai da sata da asiri da sauransu, a tsakanin watannin Maris da Afrilu.

Ya kara da cewa, ayyukan rundunar sun kai ga nasarar ceto mutane 4 da aka sace da kuma gano nau’ika daban-daban na bindigogi da alburusai 31.

A cewarsa, sauran abubuwan da aka gano sun hada da kwanson alburusai 53 da motoci 3 da babura masu kafa 3 guda 6 da kuma babura 2 da dai sauran tarin wasu abubuwa.

Ya kuma yabawa goyon bayan da rundunar ta samu daga masu ruwa da tsaki a fannin tsaro, bisa irin nasarar da ayyukansu ke samu a fadin jihar. (Fa’iza Mustapha)