logo

HAUSA

An gudanar da zanga-zangar adawa da ayyukan BH a Kamaru

2022-05-06 10:45:13 CMG Hausa

Daruruwan jama’a ne suka fita domin zanga-zangar adawa da ayyukan kungiyar ’yan ta’adda ta BH a lardin Arewa Mai Nisa na Kamaru a jiya Alhamis.

Masu zanga-zangar da galibinsu suka fito daga yankin Tourou, sun taro ne a gaban ofishin gwamnati dake Mokolo, domin kira ga gwamnatin ta kara matsa kaimi a kokarinta na dakile ayyukan kungiyar.

Wani daga cikin masu zanga-zangar mai suna Souleyman Mohamed, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, tun daga shekarar 2014 yankin Tourou ke fama da ayyukan BH. Lamarin da ya kai ga kisa da sace-sacen mutane a kusan kowacce rana, inda kuma muggan ayyuka suka karu a baya bayan nan. Yana mai cewa, suna son gwamnati ta tabbatar da tsaro a yankin.

Rahotannin tsaro sun bayyana cewa, cikin watan da ya gabata, an kashe gomman mutane tare da sace kusan wasu 20 a yankin na Tourou. (Fa’iza Mustapha)