logo

HAUSA

Jami’an lafiya na kasar Sudan ta Kudu da takwarorinsu Sinawa sun karawa juna sani game da muhimmancin tsaftar hannu

2022-05-06 10:48:06 CMG Hausa

Jami’an lafiya na kasar Sudan ta kudu da takwarorinsu na Sin, sun hada kai wajen karawa juna sani kan muhimmancin kula da tsaftar hannu a cibiyoyin lafiya, a wani yunkuri na kandagarki da dakile cututtuka masu yaduwa. Wannan ya zo ne a daidai ranar da hukumar lafiya ta duniya ta ayyyana domin wayar da kai game da muhimmancin tsaftar hannu a fadin duniya.

Mario Dumba, jami’in dake aiki a sashen tiyata na asibitin koyarwa na Juba, ya yabawa mambobin tawaga ta 9, ta jami’an lafiya Sinawa, bisa amfani da suka yi da wannan rana wajen wayarwa sauran jami’an lafiya da marasa lafiya kai, game da muhimmancin wanke hannu.

A shekarar 2009 ne hukumar WHO ta ayyana ranar tsaftar hannu ta duniya inda takenta ke mayar da hankali kan muhimmancin tsaftar hannun wajen tabbatar da lafiya da aminci.

Tun bayan samun ’yancin kan kasar Sudan ta Kudu a shekarar 2011, jerin tawagogin likitoci Sinawa ke kula da marasa lafiya tare da horar da takwarorinsu na kasar. (Fa’iza Mustapha)