logo

HAUSA

Jakadan Sin a Sao Tome da Principe ta halarci bikin bude kamfanin sarrafa rogo na Margarida Manuel

2022-05-06 20:13:21 CMG Hausa

A jiya Alhamis, jakadan Sin a Sao Tome da Principe Xu Yingzhen, ta halarci bikin bude kamfanin sarrafa rogo na Margarida Manuel, kamfanin da tawagar jami’an fasahar noma ta kasar Sin ta tallafa wajen gyara shi kasar.

Jakada Xu tare da ministan noma na Sao Tome da Principe Francisco Martins dos Ramos ne suka jagoranci bude kamfanin da aka yiwa kwaskwarima cikin hadin gwiwa. (Saminu)