logo

HAUSA

Amurka kasa ce da har kullum take kitsa karairayi

2022-05-06 13:32:21 CMG Hausa

Kwanan nan ne ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar da wata sanarwa a shafinta na Intanet, inda ta shafawa wasu jami’an gwamnati gami da kafafen yada labaran kasar Sin bakin fenti. Tana mai cewa, wai sun kara ruwaito “bayanan bogi” na kasar Rasha kan batun Ukraine, al’amarin da ya taimakawa Rasha daukar matakan soja kan Ukraine.

A cikin sanarwar, laifin da Amurka ta dorawa kasar Sin, rahotanni ne bisa gaskiya da kasar Sin ta ruwaito kawai. Alal misali, sanarwar ta zargi kasar Sin cewa, wai ta kara gishiri kan “bayanan karya” da Rasha ta fitar, wato Amurka ta mallaki dakunan gwajin halittu a Ukraine. Amma hakikanin gaskiya ita ce, tun tuni ita Amurka ta amince da wannan.

A watan Nuwambar shekara ta 2021, Amurka ta gabatar da bayanin aikinta ga babban taron kasashen da suka rattaba hannu kan “yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba”, inda ta amince cewa ta mallaki wasu dakunan gwajin halittu 26 a kasar Ukraine. A watan Maris din bana, ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar da takardar dake nuna cewa, tana da “wuraren hadin-gwiwa” 46 a cikin Ukraine.

Sanarwar ta kara da cewa, game da yadda kasar Sin ta yi don kara ruwaito “rahotannin karya” na Rasha, za’a iya samun karin haske ta jaridar New York Times da sauran wasu kafafen yada labarai, al’amarin da ya sake shaida cewa, jami’an gwamnati gami da kafofin watsa labarai na Amurka ne suke rika yada “labaran bogi” kan batun Ukraine, kuma ita kasar Sin tana jin radadi a jikinta saboda shafa mata bakin fenti da Amurka ta yi.

Amurka, wadda ita ce ta kirkiro rikicin Ukraine, ta rasa imani a duk fadin duniya tun tuni. Duk wani abun da ta yi na shafawa kasar Sin bakin fenti, ya sake shaida mummunan laifin da ita kanta ta aikata. (Murtala Zhang)