Ganin labarin malam Lv Tiezhi da dansa, ganin al’adar jirgin leda ta Sin
2022-05-05 09:35:42 CMG Hausa
Jirgin leda, daya ne daga cikin al’adun gargajiya na kasar Sin, wanda ke da tarihi mai tsawon shekaru fiye da dubu biyu. Jirgin leda na da nau’ika daban daban. Kuma yana tashi sama ne bisa amfani da karfin iska. Yana da ban sha’awa. Wani sabon abu aka kirkiro kan kera jirgin leda, bisa tushen gargajiya?
Akwai kungiyoyi daban daban na masu kera jirgin leda a kasar Sin, Lv Tiezhi yana cikin wata kungiya mai suna Jinma. Kungiyar Jinma ta samu sunanta ne saboda kwarewa kan zane-zane masu kyau. Ban da wannan, malam Lv ya fada min cewa, ana bukatar wani abu na musamman don kera jirgin leda mai kyau.
A shekarar 1984, Lv Tiezhi ya koyi fasahohin kera jirgin leda daga Guan Baoxiang, da kera jirgin leda mai salon kungiyar Jinma. Bayan wasu shekaru, ya zama kwararren mai kera jirgin leda. Amma bayan rasuwar malaminsa,sai ya rage shi kadai tilo a kungiyar Jinma. Don haka, yana da sabon tunani kan raya al’adar jirgin leda.
Tun daga shekarar 2009, Lv Tiezhi ya fara yada al’adar jirgin leda ga jama’a, don sa kaimi ga karin jama’a su fahimci al’adar. Kana ya ziyarci kasashe fiye da 10, don koyar da ilmin jirgin leda ga dalibai daga kasa da kasa, inda ta hakan, ya yada al’adar jirgin leda ta Sin zuwa sassan duniya.
A cikin gidan malam Lv, akwai jirgin leda iri iri da ya kera da kansa, ciki har da salon kifin tarwada, da kaguwa, da tsutsun Swallow da sauransu. Jirgin leda irin kama da kifin tarwada yana da gemu da idanunsa, kuma yana da wutsiya mai tsayi a kasa, kifin ya na iyo a cikin ruwa. Jirgin leda irin kama da kaguwa ya yi kamar yin rayuwa a cikin ruwan teku.
Kana malam Lv ya yi bayani game da jirgin leda irin gargajiya na birnin Beijing. Ya ce,“Jirgin leda irin na Beijing, sunanshi Sha Yan. A hakika da farko akan kira shi Zha Yan, wato an yi amfani da gora don kera jirgin kamar tsutsun Swallow, wanda keda wutsiya kaman almakashi, da reshe da kuma kai, saidai ana kiransa da Sha Yan irin na Beijing.”
Ban da su, akwai wasu jirgin leda masu kama da bututu ne, ana saka igiya a kan shi, sai iska ta shiga cikin jirgin ledar, ta haka jirgin leda ya iya tashi zuwa sama.
Kana akwai jirgin leda masu salon Beijing Opera. Iska tana shiga cikin jirgin ledar, sai ya tashi shi zuwa sama.
Saidai malam Lv ya fada yadda aka kera wani jirgin leda. Ya ce,“Wannan shi ne gora. Da farko dai zan kone shi kadan don lankwasa shi, ki saka launukan da kike so kan zanen. Bayan haka, sai mu ci gaba da kera jirgin leda tare.”
Bayan malamin malam Lv Tiezhi ya rasu a shekarar 2000, shi ya dauki babban nauyi bisa wuyansa, domin babu taimakon malaminsa, amma yana bukatar taimakonsa. Yana son yin kokarin sa kaimi ga karin matasa su fahimci wannan al’ada ta gargajiya.
Yanzu Lv Tiezhi ya tsufa, amma abin farin ciki shi ne, ya samu magajin da zai ci gaba da yada al’adar jirgin leda.
Lv Yang, dan Lv Tiezhi dake da sha’awar kera jirgin leda kamar mahaifinsa.
Amma a matsayin matashi, yana da tunani na daban kan kera jirgin leda. Ya ce, mahaifinsa ya kan kera jirgin leda irin na gargajiya, lokacin da ya koyi mini kera jirgin leda, irin na gargajiya ne. Amma Lv Yang yana son shigar da wasu sabbin abubuwa cikin jirgin leda, yana son shigar da abubuwan da matasa ke so kan jirgin leda.
Lv Yang yana shawa’ar fasahohin kamfuta, inda ya zama ma’aikaci mai fasahar kamfuta bayan ya gama jami’a. A shekarar 2014, ya yi watsi da aikinsa, don fara koyon fasahohin kera jirgin leda, amma, bai yi watsi da fasahohin kamfuta ba.
Abin da Lv Yang ya kirkiro shi ne zane-zane da siffar jirgin leda na zamani.
Lv Yang yayi dan bayani game da sabon jirgin leda da ya kera. Ya ce, yana son kara kyautata salo da launin jirgin ledar. Wannan jirgin ledar yayi kaman babbar kofar Yongding ta Beijing. An kafa kofar Yongding, domin tabbatar da tsaron birnin Beijing. Bayan an bude wannan kofa, ana iya ganin wasu manyan gine-gine masu launuka dake alamanta Beijing. Don haka, jirgin zai zama mai kyaun gani.
A hakika dai, malam Lv Tiezhi ya yi shakkar kera irin wannan jirgin leda da dansa ya tsara. Domin a baya, babu wanda ya taba amfani da salon gini don kera jirgin leda a Beijing. Bayan dansa ya gama yin zane-zanen, malam Lv Tiezhi ya duba ya ga shi ya kirkiro sabbin abubuwa, tunaninsa irin na matasa ne. Don haka, ana iya gadon wannan al’adar gargajiya, da kuma samun ci gaba.
A halin yanzu, Lv Yang ya kasance matashi memban kungiyar Jinma. Ban da kirkiro sabon jirgin leda, ya kan bada horo a wasu makarantu. Zuwa yanzu, ya gabatar da horo fiye da dubu daya a cikin shekaru 5 da suka wuce. Kamar mahaifinsa, yana kokarin yada al’adar jirgin leda. A dalilinsu biyun, al’adar jirgin leda ta gargajiya, ta ci gaba da samun karbuwa a kasar Sin.
Da farko na dauki jirgin leda a matsayin abin wasa, amma bayan haduwata da malam Lv da dansa, tunanina ya sauya. Bayan jin labarinsu, al’adar jirgin leda ta yi matukar burge ni. Ganin yadda jirgin leda ke tashi sama, na fahimci cewa, wannan al’ada na da ma’ana matuka.(Zainab)