logo

HAUSA

Babban sakataren MDD ya yi alkawarin nuna cikakken goyon baya ga kokarin Najeriya na yaki da ta’addanci

2022-05-05 10:37:44 CMG HAUSA

 

Jiya ne, Antonio Guterres, babban sakataren MDD ya bayyana a birnin Abuja, hedkwatar kasar Najeriya cewa, zai baiwa gwamnatin Najeriya cikakken goyon baya, kan kokarin da take yi na yaki da ta’addanci. MDD ta yi kira ga kasashen duniya, da su kara bai wa Najeriya taimakon jin kai, a kokarin taimakawa farfado da wuraren da hare-haren ta’addanci suka shafa a kasar.

A yayin taron manema labaru na hadin gwiwa da suka halarta da shugaba Muhammadu Buhari a wannan rana, Guterres ya ce, kawar da ta’addanci baki daya na bukatar daukar matakan soja masu karfi da ma gudanar da tsarin karba-karba da sauya tunanin tsoffin mayakan da suka bar tsattsauran ra’ayi, ta yadda za a ba su kyakkyawan fatan komawa cikin al’umma. Har illa yau MDD ta yi kira ga kasashen duniya, da su kara bai wa Najeriya dalar Amurka miliyan 350, baya ga dalar Amurka biliyan 1.1 da MDD ta shirya ba ta a matsayin taimakon jin kai, a kokarin kara karfin taimakawa wuraren da hare-haren ta’addanci suka rutsa da su a Najeriyar.

Guterres ya kara da cewa, MDD ba za ta sauya goyon bayan jin kai da take baiwa Najeriya da sauran kasashen wadanda suke daidaita mabambantan kalubaloli ba.

A nasa bangaren kuma, shugaba Buhari ya ce, gwamnatin Najeriya tana tsugunar da ’yan gudun hijira bisa shirin da ta tsara da kuma sauya tunanin dakaru masu tsattsauran ra’ayi wadanda suka mika wuya. (Tasallah Yuan )