logo

HAUSA

Matasa, kashin bayan ci gaban kowace al’umma

2022-05-04 10:15:07 CMG Hausa

Matasa su ne kashin bayan ci gaban kowa ce al’umma, wannan ne ma ya sa mahukuntan kasar Sin suka kebe ranar 4 ga watan Mayun kowace shekara, a matsayin Ranar Matasa ta kasa. Kuma saboda muhimmancin matasa ga ci gaban kowace kasa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha nanata cewa, idan har yara manyan gobe suna da manufofi da kwarewa da nauyi, hakika kasa tana da makoma da kuma fata mai kyau.


Ita dai wannan rana, ta samo asali ne, a ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919, lokacin da wasu matasa masu kishin kasar Sin suka shirya gangamin yaki da mulkin danniya da aka yi wa kasar.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, inganci da kokarin matasa, yana shafar matakan cimma mafarkin kasar Sin. Baya ga kasancewarsu jigon ci gaban kasa, matasa na iya zama wata gada dake sada zumunta, da musanyar kwarewa da fasashohi, da al’adu da kasuwanci da sauransu tsakanin kasashe da al’ummominsu. 


A kwanakin nan ne ma, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani ta farko kan matasa, mai taken: “Matasan kasar Sin a sabon zamani” inda takardar ta bayyana yadda matasan kasar Sin suke rayuwa cikin yanayi mai kyau da ba a taba gani ba a tarihin kasar Sin, ta hanyar more kyakkyawan yanayi na ci gaba da tarin damammaki na kyautata sana’o’insu.

Tun bayan barkewar annobar COVID-19, sama da jagororin matasa dubu 320 da matasa sama da miliyan 5.5 ne suka shiga aikin yaki annobar. An samu bayyanar rukunonin matasa masu basira a fannonin kimiyya da fasaha, wadanda ke da gogewa a duniya, wadanda har suka yi nasarar jagorantar manyan ayyuka na kimiyya da fasaha kamar kumbunan "Tiangong (Fadar dake Sararin Samaniya)", da "Tianyan (Idon Sararin Samaniya)" da "Tianwen (Binciken Sararin Sama A Can Can Can)".


A fagen wasannin Olympics, da na Asiya da sauran al'amuran kasa da kasa kuwa, matasan kasar Sin sun kasance a kan gaba a ko da yaushe, wajen ganin sun lashe lambobin zinari da na azurfa.

Matasa dake tsakanin shekaru 18 zuwa 30, sun zama wani babban karfi da ke shiga a dama da su a cikin harkokin wasannin kankara da na dusar kankara, inda adadin matasan da suka shiga wannan harka, ya kai kaso 37.3 cikin 100, adadi mafi girma a tsawon shekaru. (Ibrahim Yaya, Saminu Hassan)