logo

HAUSA

Sakatare janar na MDD ya kai ziyara Nijeriya

2022-05-04 15:54:14 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya fara ziyara a Nigeria, bayan wadda ya kai jamhuriyar Niger. Jigon ziyarar tasa a kasashen biyu na yammacin Afrika shi ne, matsalolin tsaro da na jin kai da yankin Sahel ke fama da su.

Antonio Guterres ya tashi daga Niger a ranar 3 ga wata, inda kai tsaye ya isa birnin Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, haka kuma mai makwabtaka da iyaka da kasashen Niger da Kamaru da Chadi. Yankin dai ya kasance dadadden wuri da rassan kungiyoyin BH da na IS na yankin yammacin Afrika ke aiwatar da muggan ayyukansu.

A kuma ranar, Sakatare janar din ya gana da gwamnan jihar na Borno da wasu iyalai mazauna yankin da hare-haren ‘yan ta’addan ya shafa.

Bayan nan, Antonio Guterres zai wuce Abuja, babban birnin kasar, domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo. Har ila yau, yayin da yake Abujan, Antonio Guterres zai ziyarci kabarin wadanda harin bam na ginin MDD a shekarar 2011 a Abuja, ya rutsa da su. (Fa’iza Mustapha)