logo

HAUSA

Gwamnatin Somaliya ta yi Allah wadai da harin da aka kai sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na AU a Somaliya

2022-05-04 15:23:48 CMG Hausa

A ranar 3 ga watan Mayu, agogon wurin ne, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta al-Shabaab a Somaliya, ta kai hari kan wani sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka da ke jihar Shabelle na tsakiyar Somaliya. A cewar kafar yada labaran kasar, kungiyar ta halaka sojojin Burundi fiye da 170 da ke sansanin. Kuma ya zuwa yanzu, jami'ai ba su tabbatar da wadannan bayanai ba.

Gwamnatin Somaliya ta fitar da wata sanarwa, inda a cikinta ta yi kakkausar suka kan harin. Har yanzu dai, tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka a Somaliya, ba ta mayar da martani kan lamarin ba.

An yi imanin cewa, kungiyar al-Shabaab na da alaka da kungiyar al-Qaeda, kuma tana neman hambarar da gwamnatin Somaliya. A shekarar 2011, dakarun kungiyar tarayyar Afirka, sun yi nasarar fatattakar mayakan na al-Shabaab daga Mogadishu, amma har yanzu kungiyar masu tsattsauran ra'ayin, na rike da yankuna da dama na yankunan karkarar Somaliya inda suke yawaita kai hare-hare a kusa da Mogadishu da makwabciyarta kasar Kenya.(Ibrahim)