logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijer ya wallafa sharhi a babbar kafar yada labaran Nijer

2022-05-03 21:00:54 CMG Hausa

A ranar 1 ga watan Mayu, jakadan kasar Sin a Nijer, Jiang Feng, ya wallafa wani sharhi mai taken, “Kasar Sin ta sa kaimi wajen bin tafarkin yaki da talauci" a babbar kafar yada labarai ta kasa da kasa ta Nijer, inda aka gabatar da bayanai game da nazarin da kasar Sin ta yi, da hakikanin aiwatar da shirin, da kuma kwarewar da ta samu a fannin yaki da talauci.

Jiang Feng, ya bayyana cewa, a bisa tsarin bincike na dogon lokaci, da aiwatarwa, kasar Sin ta sa kaimi wajen bin tafarkin shirin yaki da fatara, inda ta cimma muhimman sakamako. Akwai dalilai masu tarin yawa da suka tabbatar da hakan. Na daya shi ne, bin salon shugabanci karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. Na biyu, aiwatar da hakikanin dabarun shirin yaki da talauci. Na uku, gina wani managarcin tsari wanda zai ba da tabbacin wajen hana sake fadawa cikin yanayin kangin talauci. (Ahmad)