logo

HAUSA

Gwamnatin wucin gadi a Mali ta soke yarjejeniyar tsaron da ta kulla da Faransa

2022-05-03 20:25:16 CMG Hausa

Gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali ta sanar a ranar Litinin cewa, ta soke yarjejeniyar tsaro da ta kulla da kasar Faransa, inda ta kafa hujjar cewa, a lokuta da dama, dakarun tsaron kasar Faransa sun sha saba dokokin dake shafar iko da sararin samaniyar kasar.

Abdoulaye Maiga, kakakin gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, a lokuta da dama da suka gabata, gwamnatin kasar Mali ta sha bayyana takaicinta game da sakwarkwacewar yanayin hadin gwiwar dake tsakanin sojojin kasar da Faransa.(Ahmad)