logo

HAUSA

Agaji Chaibou: Ina son kara bada gudummawa ta wajen samun fahimtar juna tsakanin mutanen Nijar da Sin

2022-05-03 14:30:11 CMG Hausa

Agaji Chaibou, dan asalin jihar Diffa ne dake Jamhuriyar Nijar, wanda a yanzu haka yake aiki a wani kamfanin hako albarkatun man fetur na kasar Sin dake Nijar, mai suna CNPC Dagang Niger Engineering.

A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Agaji Chaibou ya yi tsokaci kan yadda ya koyi harshen Sinanci, gami da fahimtarsa kan halayen mutanen kasar.

Ya kuma bayyana cewa, yana son bayar da gudummawa wajen kara samun fahimtar juna tsakanin al’ummomin Nijar da Sin. (Murtala Zhang)