logo

HAUSA

FIFA ta ci tarar Senegal da Najeriya

2022-05-03 16:58:39 CMG Hausa

A ranar 2 ga watan Mayu, hukumar shirya gasar wasannin kwallon kafa ta kasa da kasa FIFA, ta sanar da hukunta wasu kasashe da suka hada da Senegal da Najeriya, bayan samunsu da saba dokoki a lokacin wasannin share fagen gasar cin kofin duniya ta 2022.

Bayan nazarin gomman laifukan da aka tafka a lokacin wasannin share fagen gasar cin kofin duniya, wanda aka fara tun a farkon wannan shekarar, kwamitin da’a na FIFA, ya fitar da jerin hukunce-hukunce da aka gabatar a ranar 2 ga wata, inda aka ci tarar kasar da ta zama zakara a gasar kwallon kafan Afrika wato kasar Senegal kimanin kudi Swiss francs 175,000, sakamakon laifuka da dama da ta aikata. Daga cikin laifukan rashin da’ar da ta aikata sun hada da taron dandazon magoya bayan kungiyar wasa na kasar da suka yi a tsakiyar filin wasa, da yin amfani da kwalaye masu dauke da kalaman batanci, da gazawa wajen tabbatar da bin doka da oda a filin wasan.

A ranar 29 ga watan Maris, a lokacin gabatar da zagaye na biyu na wasan rukuni na uku na gasar share fagen cin kofin duniya na kasashen Afrika wanda aka gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya, inda aka tashi wasan 1-1 tsakanin Najeriya mai masauki baki da Ghana, wanda shi ne jimillar maki 1-1 da kasar ta samu a zagaye na biyu, sai dai an fidda Najeriyar sakamakon karancin yawan kwallayen da ta zura. Lamarin da ya sa kasar ta rasa damar shiga gasar neman cin kofin duniya a karo na farko tun a shekarar 2006. Bayan buga wasan, magoya bayan kungiyar kasar sun tada bore a filin wasan dake Najeriyar, inda ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla don daidaita al’amurra.

Hukuncin da FIFA ta zartar ta ce, sun hada da laifin gaza bin dokokin tabbatar tsaron lafiya, da gaza tabbatar da bin doka da oda a filin wasan, da tada rikici a filin wasan, da jefa abubuwa a filin wasan. A sakamakon hakan, an ci tarar hukumar shirya wasanni ta Najeriya kudin da ya kai Swiss franks 150,000. Kuma Najeriyar za ta buga wasanta na gaba na cikin gida da kasar Senegal ba tare da halartar ‘yan kallo ba. (Ahmad)