logo

HAUSA

Shugaban Burundi ya ba da lambar yabo ga masanin Sin a bikin ranar ma'aikata ta duniya

2022-05-03 16:04:11 CMG Hausa

Jiya ne, shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye, ya ba da lambar yabo ga fitattun ma'aikata da kungiyoyi, ciki har da Yang Huade dan kasar Sin, yayin da kasar ta Burundi ke bikin ranar ma'aikata ta kasa da kasa.

Ndayishimiye ya ce, kwararre kan harkar noman shinkafa na kasar Sin ma yana cikin wadanda ke yi wa kasarmu muhimman ayyuka.

Shugaban ya yabawa Yang Huade, wanda ya ce, za a iya girbe tan 10 na shinkafa a kadada daya kacal na filin gonaki. Ya kara da cewa, Yang ya ba da gudummawa matuka ga cibiyar binciken shinkafa ta Gihanga da ke lardin Bubanza na kasar Burundi.

Ndayishimiye ya kuma yi nuni da cewa, an san Yang a wasu wurare kamar Karusi da Gitega da ake noman shinkafa, saboda yadda yake taimakawa masu noman shinkafa da ilimi da kuma dabarunsa.

An yi bikin ranar ma'aikata ta duniya a filin wasa na Umuco da ke garin Muyinga na lardin Muyinga da ke arewa maso gabashin kasar Burundi. (Ibrahim)