logo

HAUSA

Guterres ya bukaci a tallafawa Nijer yakar ta’addanci

2022-05-03 15:36:25 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD, Antonio Guterres, ya bukaci kasa da kasa su zuba jari don karfafawa dakarun sojojin Nijer gwiwa a ayyukan yaki da ta’addanci.

A taron manema labarai da aka gudanar tare da shugaban kasar Nijer, Mohamed Bazoum, mista Guterres ya ce, hare-haren ta’addanci suna ci gaba da karuwa a yankin Sahel, kuma suna kara yaduwa zuwa yankunan kasashen dake daura da tekun Guinea, ya ce ya zama tilas kasa da kasa su fahimci cewa, al’amarin ba batu ne da ya shafi shiyyar ko kuma Afrika kadai ba, sai dai batu ne dake barazana ga duniya baki daya.

Ya ce, “Wajibi ne kasa da kasa su zuba cikakken jari wajen karfafawa ayyukan dakarun sojojin jamhuriyar Nijer, zan ci gaba da mika bukatun neman tara kudade da karin albarkatun da ake bukata domin tinkarar wadannan kalubaloli.”

Guterres ya ce, Nijer ba za ta iya tinkarar wadannan kalubaloli ita kadai ba, inda ya yi nuni da cewa, kungiyoyin tarayyar Afrika AU, da G5 Sahel, da ECOWAS, muhimman ginshikai ne ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ci gaban shiyyar.

G5 Sahel kungiya ce ta shiyya, kana babbar kungiyar diflomasiyya ce da ta kumshi kasashen Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da Nijer, yayin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, kungiya ce mai kumshe da kasashen yammacin Afrika 15, daga cikinsu akwai kasashen Mali, Nijer da Najeriya.(Ahmad)