Bikin sayar da kayayyakin Afirka ya nuna burin Sin na tabbatar da cin moriyar juna
2022-05-02 21:04:07 CMG Hausa
Wasu mintuna 5 da suka wuce, na yi kai-komo tsakanin wasu nau’o'in waken gahawa na Kenya, da Habasha, da Rwanda, kafin na zabi daya daga cikin su, na zabi waken da aka samar da shi daga yankin Muranga na kasar Kenya, don ya zama kyautar karamar sallah, da zan ba kaina.
Na sayi waken ne ta wani dandalin sayar da kayayyaki ta yanar gizo na kasar Sin. A kwanakin nan, ana gudanar da “bikin sayar da ingantattun kayayyakin kasashen Afirka” a dandali daban daban na kasar Sin. Kawai na danna wani link da ya bayyana a wayar salula ta, sai na ga hoton bidiyon yadda wasu ‘yan Afirka, da Sinawa suke kokarin gabatar da wasu nagartattun kayayyakin Afirka cikin himma: Miyar yaji ta Rwanda, da lu’u-lu’un kasar Tanzania, da man koko na Ghana, da darduman kasar Morocco, da dai sauransu. Kusan ana iya samun kayayyakin dukkan sassan nahiyar Afirka a wajen wannan biki.
Watakila za ku so ku yi tambaya: Me ya sa Sinawa ke son kafa wani bikin musamman ma domin su rika sayen kayayyakin kasashen Afirka?
Da farko dai, sun yi haka ne don cika alkawarin da suka yi. A wajen taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a bara, inda shugaban kasar Sin ya gabatar da manyan ayyuka guda 9 game da hadin kan Sin da Afirka, ciki har da habaka hadin gwiwar bangarorin 2 ta fuskar tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani, da ta kasuwanci. Yanzu, ta hanyar gudanar da wannan biki na sayar da kayayyakin Afirka, an daidaita fasahohi tsakanin dandalin kasuwanci na kasashen Afirka da na Sin, da habaka ciniki a tsakaninsu. Hakan ya dace da burin Sin na aiwatar da “manyan ayyuka 9” da ta gabatar.
Na biyu shi ne, kawar da shingaye, ta yadda tsarin samar da kayayyaki zai gudana yadda ake bukata a duniya. Kasancewar wani muhimmin bangare na tsarin samar da kayayyakin masana’antu na duniya, kasar Sin ba ta son ganin annobar COVID-19, da wutar yaki, da jajayya a fannin siyasa sun zama shingayen da suka hana zirga-zirgar kayayyakin da ake bukata a kasuwannin duniya. Saboda haka kasar na kokarin bude kofarta, da hadin gwiwa da sauran kasashe, don tabbatar da gudanar da tsarin samar da kayayyaki, tare da ba kasuwannin kasa da kasa cikin wani yanayi mai kyau.
Ban da haka, wannan biki na sayar da kayayyakin kasashen Afirka ya nuna babban burin kasar Sin, yayin da take hulda tare da sauran kasashe, wato tabbatar da moriyar juna. Sinawa sun san cewa, manufar barin wani bangare ya ci riba shi kadai, yayin da bangare na daban ke yin hasara, tana haifar da rikici ne kawai. Kana yunkurin tabbatar da moriyar juna shi ne tushen zaman lafiya, da hadin kai, da kuma ci gaba. Wannan ra’ayi ya sa kasar Sin bude kofarta, ta hanyar bikin sayar da kayayyakin Afirka, da bikin baje kolin kayayyakin ketare, da dai makamantansu, inda take gayyatar ‘yan kasuwan kasashe daban daban su zo kasar Sin su sayar da kayayyakinsu. Ta wannan hanya, ‘yan kasuwan kasashen waje sun samu riba, kasar Sin ita ma ta janyo jarin waje, da habaka ciniki, da kulla huldar hadin kai, gami da ciyar da tattalin arzikinta gaba. Burin tabbatar da moriyar juna ya cika ke nan.
Abokaina, ko kuna da wani kayan da kuke son sayar da su a kasar Sin? A hanzarta a fara daukar mataki, don Sinawa na maraba da zuwanku. (Bello Wang)