logo

HAUSA

Rikicin Ukraine yana kara haifar da tarin matsaloli a Afrika

2022-05-02 15:27:26 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, rikicin dake ci gaba da faruwa a kasar Ukraine yana kara haifar da matsalar abinci, da makamashi da matsalolin kudi a kasashen Afrika.

A yayin taron ‘yan jaridu na hadin gwiwa da shugaban kasar Senegal Macky Sall, mista Guterres ya ce, ya kafa wata kungiyar kai dauki gaggawa ta kasa da kasa domin karfafa gwiwar hukumomin MDD, da bankunan raya ci gaba, da sauran kungiyoyin kasa da kasa, don rage mummunan tasirin da rikicin ke haifarwa, musamman a kasashen Afrika.

Guterres, ya bukaci a janye dukkan shingayen hana fitar da kayayyaki da aka sanya da ba su dace ba, domin a samu damar bude kasuwannin hada-hadar abinci da makamashi, da kuma daidaita farashin abinci.

Ya ce, ba zai yiwu a warware hakikanin matsalolin karancin abinci ba, idan ba a sake farfado da samar da abinci a kasar Ukraine ko kyautata aikin samar da abinci da takin zamani ga kasuwannin duniya daga kasashen Rasha da Bekarus ba. (Ahmad)