logo

HAUSA

Hukumar NDLEA a Najeriya ta kwace tarin magungunan jabu

2022-05-02 15:37:39 CMG Hausa

Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ko NDLEA a takaice, ta kwace katan 47 na maganin kashe radadin ciwo nau’in tramadol na jabu, mai kunshe da kwayoyi miliyan 2.3 a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar.

Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, kakakin hukumar Femi Babafemi, ya ce sun cafke mutum guda da ake zargi da safarar kwayoyin, yayin wani samame da jami’an NDLEAn suka kaddamar a kan babbar hanyar jihar ta Kaduna.

Babafemi ya ce an kuma kama mutumin da ake zargi, da kwalaben maganin tari nau’in codeine kusan 3,000, maganin da tun a shekarar 2018 gwamnatin Najeriya ta haramta shigar da shi kasar, la’akari da yadda wasu ke amfani da shi a matsayin kayan maye.

Wata kafar watsa labarai, ta hakaito sakamakon wani bincike da hukumar kididdigar kasar ta gudanar a shekarar 2020, dake nuna cewa, akwai ‘yan Najeriya miliyan 14.3, kimanin kaso 14.4 bisa dari na daukacin ‘yan kasar, dake tsakanin shekarun haihuwa 15 zuwa 64, masu ta’ammali da miyagun kwayoyi. (Saminu)