logo

HAUSA

Guterres ya yi kira ga gwamnatocin Mali da Guinea da Burkina Faso da su gaggauta komawa ga tsarin kundin mulki

2022-05-02 15:17:52 CMG Hausa

 

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Mali, da Guinea da Burkina Faso, da su gaggauta komawa tsarin kundin mulki da doka ta tanada.

Mr. Guterres ya yi kiran ne a jiya Lahadi, yayin wani taron manema labarai da ya halarta, tare da shugaban kasar Senegal Macky Sall, inda ya ce abu ne mai muhimmanci a nacewa gudanar da shawarwari tare da mahukuntan kasashen 3, domin hanzarta komawa bin doka da oda.

Babban jami’in na MDD, ya kuma bayyana damuwa game da halin da yankin Sahel ke ciki game da tsaro, ya kuma yi alkawarin ci gaba da mara baya ga manufar karfafa ayyukan wanzar da zaman lafiya, da yaki da ta’addanci a sassan nahiyar Afirka, karkashin tallafin kungiyar AU da MDD.

Daga nan sai ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su tallafawa kasashen yankin yammacin Afirka, ta yadda za su iya shawo kan kalubalen tsaro tun daga tushe.

Mr. Guterres ya isa birnin Dakar, fadar mulkin kasar Senegal ne da yammacin ranar Asabar, daga bisani kuma zai ziyarci janhuriyar Nijar da tarayyar Najeriya. (Saminu)