logo

HAUSA

Rikicin Rasha da Ukraine na kawo tasiri ga nahiyar Afirka

2022-05-01 16:25:34 CMG Hausa

Rasha, babbar kasa ce dake fitar da man fetur, da alkama, da takin zamani, da sauran kayayyakin masarufi, yanzu haka rikici ya barke tsakanin Rasha da Ukraine, a sanadin haka wasu kasashen yamma sun kakkabawa Rasha takunkumi, lamarin ya riga ya kawo mummunan tasiri ga zaman rayuwar al’ummun kasashen Afirka, musamman ma ga aikin samar da isasshen hatsi a nahiyar.

Alkaluman da hukumar kula da hatsi da aikin gona ta MDD ta fitar sun nuna cewa, daga shekarar 2018 zuwa ta 2020, kaso 32 bisa dari na alkamar da kasashen Afirka ke shigo da su daga kasashen ketare na fitowa ne daga kasar Rasha, sannan kaso 12 bisa dari daga kasar Ukraine, inda kasashen Somaliya da Benin suke shigo da kusan dukkanin alkama daga wadannan kasashe biyu wato Rasha da Ukraine. Ban da haka kuma, hukumar kula da shirin samar da hatsi ta MDD ta bayyana cewa, matsalar fari na kara tsananta a kasashen Kenya da Habasha da Somaliya, sakamakon karancin ruwan sama, an yi hasashen cewa, al’ummun kasashen da yawansu ya kai miliyan 20 za su fuskanci matsalar yunwa a bana.

Kan batun, masanan kasashen Afirka da abin ya shafa sun yi tsokaci cewa, ya dace kasashe daban daban dake nahiyar Afirka su yi kokari tare domin daidaita matsalar ta hanyar daukan matakan da suka dace.(Jamila)