logo

HAUSA

Yadda ake azumi a kasar Sin

2022-04-30 23:07:26 CRI

Kamar yadda musulmai a sassan duniya suke azumin watan Ramadan, al'ummar musulmi 'yan kabilu daban daban na kasar Sin ma yanzu haka suna azumi cikin wannan wata mai tsarki. Cikin shirinmu na yau, mu samu damar tattauna tare da Abubakar Gambo Muhammad, haifaffen jihar Kano ne, wanda yanzu ke dalibta a birnin Xi'an, babban birnin lardin Shaanxi na kasar Sin, inda muka tattauna yadda yake azumi a kasar Sin da ma bambanci da aka samu wajen yin azumi a kasar da kuma cikin gida Nijeriya. 

A biyo mu cikin shirin, don jin karin haske. (Lubabatu)