logo

HAUSA

Ma'aikatan tawagar ceto sun yi kokarin ba da tabbaci ga dawowar ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-13 cikin koshin lafiya

2022-04-30 19:15:37 CMG Hausa

A ranar 16 ga watan Afrilu, yawancin Sinawa suna kallon shirye-shiryen kai tsaye a gaban talabijin, inda suke cike da fata tare da rashin sakin jiki, don zura ido kan kowane mataki na dawowar kumbon Shenzhou-13. A wannan lokaci, a bayan fage inda masu kallo ba za su iya gani ba, wasu mata suna shagaltuwa da aiki a filin saukar kumbon na Dongfeng.

Zhu Xiaolin, mamba ce ta tawagar ceto, mai kula da aikin sarrafa na'urar nuna alkibla, tana kokarin daukar hakikanin wurin da akwatin dake dawowa da ‘yan sama jannatin na kumbon zai sauka. A nata bangare, Zhang Ying, mai ba da umurni ga tafiyar tawagar ceto, tana daidaita ayyukan ceto a ofishin ba da jagoranci. Kana kuma Wang Yuzhu, ‘yar tawagar likitoci ta 'yan sama jannati, tana cikin motar daukar marasa lafiya, don zuwa wurin da akwatin kumbon zai sauka.

Da karfe 9:56 na safe, kumbon Shenzhou-13 ya sauka doron duniya yadda ya kamata. Hakan, ya sa su nuna annashuwa da walwala a karshe.

A cikin ‘yan watanni da suka gabata, sun yi ta share fage don ba da tabbaci ga tashi da saukar kumbon Shenzhou-13 cikin lafiya.

Zhang Ying ita ce mace ta farko da ta yi aikin ba da umurni ga tafiyar tawagar ceto, a filin sauka da tashin kumbuna na Dongfeng. Sassan tawagar ceto guda biyar a karkashin jagorancinta sun kasance a matsayin masu taimakawa wajen dawo da kumbon Shenzhou-13, a shirye suke su tinkari lamurra daban-daban a ko wane lokaci.

A shekara ta 2009, Zhang Ying, wadda ta samu digiri na biyu, ta shiga cikin tawagar ceto. A lokacin, mutane da yawa sun yi mata gargadi da cewa, aikin bincike da ceto yana da wahala da hadari, don haka ya fi kyau ma’aikata mata su yi aiki a ofisoshi. Amma Zhang Ying ta yi tunanin cewa, ta yi karatu na tsawon shekaru, dole ne ta je fage na gaba don yin wani abu.

"Ana gudanar da atisayen bincike da ceto a cikin jirgin sama, jirgin sama yana da kara, da kamshin mai sosai, don haka da zarar an yi atisayen, ba damar sake cin komai har tsawon rana guda, don tabbatar da ba ta suma, ko amai ba bayan ta hau jirgin saman, ta kuma kasance cikin hali mai kyau."

Da take magana game da wadannan abubuwa, Zhang Ying ta ce cikin motsin rai, "Aikin ceto abu ne mai matukar wahala, amma idan za mu iya rage wahalhalu ta hanyar fasaha, sakamakon kokarin da muke ci, ina ganin zai kasance mai kima sosai." Zhang Ying ta dage kan aikin bincike da ceto sama da shekaru goma a tawagar ceton. Ta ce, idan aka kwatanta aikin bincike da ceto da aka yi a baya, a zahiri za su iya jin cewa, karfin kasar Sin yana karuwa. Don haka a ganinta, duk aiki tukuru da ta yi a cikin ‘yan shekarun da suka gabata ya cancanci yabo sosai. Za kuma ta ci gaba da wannan aiki a nan gaba, wadannan fasahohin da ta samu za su zama taskarta mai tamani."

A ranar 16 ga watan Afrilu, lokacin da hasken rana ya haskaka filin jirgin sama, Zhu Xiaolin da sauran mambobin tawagar ceto a shirye suke, don jiran umurnin da za a ba su.

Zhu Xiaolin, wadda ta shiga tawagar ceto a shekarar 2019, ta ce, wannan shi ne karo na farko da ta hau jirgin sama domin aiki, don haka ta yi matukar damuwa da fargaba, amma da ta yi tunanin cewa aikin ta na da muhimmanci sosai, sai ta fada wa kanta cewa, kwantar da hankalin ki, kada ki yi kuskure, kuma dole ne ki kammala aikin yadda ya kamata.

Lallai aikinta yana da mahimmanci. Lokacin da kumbon Shenzhou ya sauko kasa, mabudin samun nasarar bincike da ceto shi ne, gano hanyar saukar akwatin dake dawowa da ‘yan sama jannati cikin lokaci. Kayan aikin da Zhu Xiaolin ke amfani da shi shi ne “idon” dake iya gano akwatin na Shenzhou-13. Yana iya daukar daidai matsayin akwatin a dare da rana, kana da aikewa da matsayin ga tawagar ceto cikin sauri. Bayan haka, da sauri jirgin saman binciken ya tashi zuwa wurin da aka kebe, sannan masu aikin ceto ta kasa, su ma sun taru cikin sauri zuwa wurin da aka yi hasashen sauka. Bayan akwatin ya sauka, nan da nan kungiyoyin aiki daban daban a kasar sun taru a kusa da akwatin, a daidai wannan lokacin kuma, tawagar masu aikin ceto ta sama sun sauko daga sama, don ba da hadin kai wajen gudanar da aikin. An kammala dukkan ayyukan nan a cikin minti 30.

Da take waiwayen dukkan yunkurin aiwatar da aikin, Zhu Xiaolin ta ce, ta fi jin dadi, da kuma cikawa a lokacin da ta ga an bude laimar saukar jirgi, da kuma sauke akwatin dawo da ‘yan sama jannati na sauka lafiya. A cewarta, da kyar ake iya tabbatar da wannan aiki, wato bayan akwatin ya sauka, jirgin saman ceto zai iso ba tare da bata lokaci ba, wannan ya nuna ci gaban fasahar sararin samaniya da kasar Sin ta samu, tana da alfahari kan cimma wannan nasara sakamakon ayyukan da suka yi.

A lokacin da aka harba kumbon Shenzhou-13, motocin daukar marasa lafiya ne suka dauki nauyin aikin ceto daga kasa, wadanda ke dauke da kayan aikin jinya masu yawa, ana iya kiransu ICU masu tafi da gidanka.

Wang Yuzhu, da abokan aikinta na tawagar aikin jinya ta ‘yan sama jannati su ne suka shirya na’urori, da wasu kayayyaki dake cikin motocin daukar marasa lafiya guda uku da aka shirya, domin aikin dawowar kumbon Shenzhou-13.

Tun daga watan Maris na wannan shekara, don maraba da komawar 'yan saman jannati doron duniya, akwai bukatar a kara ayyukan ba da tabbaci a fannin rayuwa kan motocin daukar marasa lafiya. Mene ne bukatun 'yan saman jannatin bayan sun dawo? Kuma ta yaya za su kasance mafiya jin dadi? Wang Yuzhu da abokan aikinta, dole ne su yi la’akari sosai kan fannonin fasahohi, da kuma rayuwa baki daya. Ta ce, domin baiwa ‘yan sama jannatin damar cin abinci mai zafi bayan dawowar su, sun sayi kukar microwave, da injin dafa ruwa. Ban da wannan kuma, sun shirya wa ‘yan sama jannatin ‘ya’yan itace kwana daya kafin dawowarsu, da saka su a cikin injin dake iya tabbatar da matsayin zafi yadda ya kamata. Haka kuma bayan sun dawo, sun ci sabbin 'ya'yan itace masu zafi daidai bukata."

Domin tabbatar da ‘yan saman jannati za su iya jin dadi da sauki a cikin motocin, Wang Yuzhu ta halarci atisayen fage sau da yawa. A lokacin atisayen na sa'o'i 9 zuwa 12, ko da yake Wang Yuzhu tana cikin mottar, amma ba ta sha ruwa ko kadan ba, don haka ba za ta yi amfani da ban daki na musamman na 'yan sama jannatin ba.

Yanzu ‘yan saman jannatin uku sun dawo Beijing, hedkwatar kasar Sin lami lafiya, Wang Yuzhu kuma ta kammala aikinta cikin nasara. Ta yi farin ciki da cewa, ta shafe shekaru da yawa tana aikin ba da tabbaci, a wannan karon, ta cika burinta na daukar hoto tare da akwatin dawo da ‘yan samman jannati na kumbon.