logo

HAUSA

Shugabannin Afrika sun halarci jana’izar ban-girma ta tsohon shugaban Kenya

2022-04-30 18:15:27 CMG Hausa

Shugabannin Afrika sun halarci jana’izar ban-girma ta tsohon shugaban Kenya mai rasuwa, Mwai Kibaki, wanda aka yi jiya a birnin Nairobi.

Shugaba Kibaki ya mutu yana da shekaru 90, a ranar 22 ga wata, bayan ya sha fama da rashin lafiya na lokaci mai tsawo, lamarin da ya jefa kasar ta gabashin Afrika cikin yanayin na makoki.

Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa da na Habasha Sahle Work Zewde da na Afrika ta Kudu Salva Kiir tare da wakilan shugabannin kasashen Uganda da Tanzania da Malawi ne suka halarci bikin jana’izar tare da shugaba Uhuru Kenyatta na Kenyar.

Shugaba Kenyatta mai masaukin baki, ya bayyana marigayi Kibaki a matsayin daya daga cikin manyan dattawan Afrika a lokacinsa.

Ya ce marigayin ne ya gina tubalin wanzuwar kasar da ma na ci gaban tattalin arzikinta.

A yau Asabar ne kuma za a binne gawar marigayi Mwai Kibaki a Nyeri dake yankin tsakiyar kasar. (Fa’iza Mustapha)