logo

HAUSA

WHO ta fitar da sama da dala miliyan 8 domin agajin jin kai a yankin Sahel

2022-04-30 17:59:24 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar da dala miliyan 8.3 daga asusunta na shirin ayyukan gaggawa, domin tallafawa mabukatan agajin lafiya miliyan 10.6 a yankin Sahel.

Ofishin hukumar a nahiyar Afrika, ya bayyana cikin wata sanarwa a jiya cewa, bisa kiyasin mutane miliyan 33.2 da ke fama da matsanancin tasirin rikici da rashin tsaro da karancin abinci da gudun hijira a yankin Sahel, asusun zai taimaka wajen bayar da ayyukan kiwon lafiya ga mutanen dake zaune a sansanonin gudun hijira da kuma wadanda barkewar cututtuka ta shafa, a kasashe 6 na yankin.

A cewar sanarwa, hukumar za ta inganta yanayin tamuwa a Burkina Faso, da karfafa jinyar masu cutar kwalara a Kamaru da samar da muhimman hidimomi ga mutane dubu 100 a Chadi da tura masana hallayar dan Adama zuwa dukkanin yankuna 10 na Mali da horar da tawagogi 4 na masu tunkarar barkewar cututtuka a Niger, tare kuma da sake farfado da ayyuka a wasu asibitoci biyu dake arewa maso gabashin Nijeriya, wadanda ke hidimtawa mutane 300,000.

WHO ta ce alkaluman kiwon lafiya a Sahel su ne mafi tabarbarewa a duniya baki daya. Haka kuma, yankin ne mafi fama da mace-macen mata masu juna biyu a duniya, inda ake samun mutuwar mata 856 cikin kowacce haihuwa 100,000, saboda rashin ingancin hanyoyin samun kiwon lafiyar mata masu juna biyu da kuma yawaitar auren wuri.

Bugu da kari, hare-haren masu dauke da makamai kan fareren hula da fari da lalacewar filaye da rashin tabbacin yanayi, na ta’azzara matsalolin miliyoyin mutane a yankin na Sahel. (Fa’iza Mustapha)