Amurka, ki mayar da kudin al’ummar Afghanistan
2022-04-30 22:18:40 CMG Hausa
Abdul Sabir dan kasar Afghanistan ne da ke rayuwa a birnin Kabul, babban birnin kasar, a kwanakin baya, ya je kasuwa don sayo wa yaransa busassun ‘ya’yan itatuwa da riguna domin karamar sallah da za a fara nan da wasu kwanaki, amma ya koma gida cikin bakin ciki, ya ce, “Ban iya sayen kome ba, ko riguna na kasa sayo wa yarana, dukkanin kayayyaki ciki har da busassun ‘ya’yan itatuwa, farashinsu sun wuce karfinmu. Amurka ta kakaba wa kasarmu takunkumi, tare da haramta mu yi amfani da kudadenmu.”
Alkaluman kididdigar da hukumomin kasa da kasa suka fitar sun nuna cewa, sama da mutane miliyan 23 a Afghanistan na bukatar agajin abinci cikin gaggawa. Bugu da kari, sama da 'yan Afghanistan miliyan 4 ne suka rasa matsugunansu. Shin alhakin wane ne? Ko shakka babu Amurka ce. A shekara ta 2001, Amurka ta kaddamar da yaki a Afghanistan bisa dalilin wai "yaki da ta'addanci". Yakin na tsawon shekaru 20 ya yi sanadin mutuwar fararen hula ‘yan Afghanistan 100,000, kuma kusan miliyan 11 sun zama 'yan gudun hijira.
A watan Agustan shekarar da ta gabata, a kokarin da take yi na daidaita manyan tsare-tsarenta a duniya, Amurka ta yi gaggawar janye sojojinta daga Afghanistan. A watan Fabrairun wannan shekara, shugaban Amurka ya sanya hannu kan wata doka, da nufin raba kusan dala biliyan 7 na kadarorin Babban Bankin Afghanistan da Amurka ta haramta, zuwa gida biyu, kuma Amurkar za ta yi amfani da rabi don biyan diyya ga wadanda suka yi hasara a lamarin ranar 11 ga watan Satumba ko kuma harin "9.11".
Amma ko al’ummar Afghanistan ne suka kai harin “9.11”, har da za a biya hasarar harin da kudadensu? Biliyoyin daloli ba su da yawa ga Amurka, amma za su iya ceton rayuwar al’ummar kasar Afghanistan.
Amurka kullum ta kan dauki kanta a matsayin abin koyi wajen kare hakkin bil Adam, amma ko ta hakan ne take kare hakkin bil Adam? (Mai zane: Mustapha Bulama)