logo

HAUSA

Tunisiya da Sin sun yi bikin mika kwalejin diflomasiyya da Sin ta gina

2022-04-29 10:56:17 CMG HAUSA

 

Kasashen Tunisiya da Sin sun gudanar da bikin mika sabuwar kwalejin diflomasiyya ta Tunisiya ta kafar intanet, wanda kasar Sin ta taimaka wajen ginawa.

Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin, Qian Keming, ya bayyana a lokacin bikin cewa, duk da mummunan tasirin annobar COVID-19, kasar Sin ta yi nasarar kammala aikin mai matukar inganci kuma cikin hanzari, lamarin da ya bada gagarumar gudunmawa wajen zurfafa huldar dake tsakanin kasashen da kuma karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

Qian ya ce, Sin da Tunisia abokan huldar juna ne, wajen gina “shawarar ziri daya da hanya daya,” kuma kasar Sin tana son hada kai da Tunisia don yin aiki tare domin tabbatar da ci gaban kasashen biyu.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Tunisiya, Othman Jerandi, ya ce aikin gina kwalejin nazarin diflomasiyyar Tunisiya, an kammala shi a watan Disambar shekarar 2021, kamfanin gine-ginen kasar Sin ya gudanar da aikin cikin shekaru sama da biyu, kana aikin wata alama ce dake kara bayyana kyakkyawar huldar abokantaka tsakanin kasashen Sin da Tunisiya. (Ahmad)