logo

HAUSA

Koshin lafiyar zuciyar uwa yayin da take dauke da ciki yana tasiri kan yaro a lokacin samartaka

2022-04-28 11:04:41 CMG HAUSA

 

Wani sabon bincike da asibitocin kula da yara na Northwestern Medicine and the Ann & Robert H. Lurie dake Chicago na kasar Amurka ya gudanar ya nuna cewa, koshin lafiyar zuciyar mahaifiya yayin da take dauke da juna biyu, na iya yin tasiri matuka kan lafiyar zuciya da jijiyoyin jinin yaro ko yarinyarta a farkon shekarun samartaka tsakanin shekaru 10 zuwa 14.

Masu binciken sun yi nazari kan fiye da iyaye mata 2,300 da yara biyu daga kasashe shida. Sun kuma samu juna biyu ne tsakanin shekarar 2000 zuwa 2006, an kuma duba yaran a shekaru 10 zuwa 14 a shekarar 2013 zuwa shekarar 2016.

Ta hanyar amfani da ma'anar lafiyar zuciya da jijiyoyin jini ta kungiyar likitoci masu kula da lafiyar zuciya da jijiyoyin jini ta Amurka, masu binciken sun raba yanayin koshin lafiyar zuciya da jijiyoyin jini na iyaye mata bisa la’akari da mizanin BMI, da hawan jini, da yanayin kitse, da matsayin glucose da shan taba a cikin makonni 28 na daukar ciki. Masu binciken sun kuma rarraba yanayin koshin lafiyar zuciya da jijiyoyin jini dangane da mizanin BMI, da hawan jini, da yawan kitse da glucose a cikin shekaru 10 zuwa 14.

Binciken ya nuna cewa, yaran da iyaye mata mafi karancin koshin lafiyar zuciya da jijiyoyin jini suka haifa, wadanda ke wakiltar kashi 6 cikin dari na iyaye mata, suna da hadarin da ya kai kusan ninki takwas mafi girma na mafi karancin koshin lafiyar zuciya da jijiyoyin jini a farkon lokacin samartaka, idan aka kwatanta da yaran da iyaye mata wadanda ke da kyakkyawar koshin lafiyar zuciya da jijiyoyin jini a lokacin da suke daukar ciki, suka haifa.

Jagorar masu binciken Dr. Amanda Perak, mataimakiyar farfesa a fannin ilimin yara da kuma rigakafi a asibitin kula da yara na Lurie da makarantar likitanci ta Feinberg ta Jami'ar Northwestern NU ta ta bayyana cewa, sabon bincikensu ya nuna cewa, yaran dake cikin wannan rukuni na iyaye mata masu fama da rashin koshin lafiyar zuciya da jijiyoyin jini, na iya zama mafi hadari ga raguwar farko na lafiyar jikin su a lokacin yarinta. Ta kara da cewa, idan za mu iya magance wadannan abubuwan da ke haifar da matsalar koshin lafiyar zuciya ga yara, muna fatan za mu iya taimaka musu wajen ganin ba su sake kamuwa da ciwon zuciya, da shanyewar jiki da kuma mutuwa da wuri ba yayin da suke girma a nan gaba.

A cewar Perak, nan ba da dadewa ba, yaran da suka shiga wannan bincike, za su manyanta, kuma a mataki na gaba, za mu yi kokarin auna koshin lafiyar zuciya da jijiyoyin jini da kuma alamun cututtukan zuciya na farko da suka gamu da su yayin da suka fara manyanta

Haka kuma, masu binciken suna shirin gano dalilan da ya sa matsalar ciwon zuciya da jijiyoyin jini yayin daukar ciki, ke iya haifar da rashin koshin lafiyar zuciya da jijiyoyin jini ga yara.